1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu manoma sun hallaka a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 29, 2020

A Najeriya 'yan bindiga sun hallaka wasu manoma biyu da kuma yin garkuwa da wasu manoman biyu da suka tarar suna aikin noma a gonakansu kusa da birinn Maiduguri na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/3hkKN
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Wani dan kato da gora suna Muhammed Bukar ya shedawa kamfanin dillacin larabai AFP da cewa sun tarar da gawawakin wadanda suka gamu da ajalinsu dauke da muggan raunukan da ke nuni da cewar an sassaresu ne da adda.

Fiye da mutun dubu 36 000 ne suka game da ajalinsu a yankin arewacin Najeriya tun daga shekarar 2019 zauke yanzu, a yayin da wasu fiye da miliyan daya suka kauracewa gidajensu sakamakon tashe tashen hankulan da ke da nasaba da ta'addanci.