SiyasaJamus
An kashe dan majalisar dattawa a Kamaru
January 12, 2022Talla
An halaka wani dan majalisa a birnin Bamenda da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Kamaru, yankin da ke fama da rikicin 'yan aware masu fafutikar kafa kasa.
An gano gawar dan majalisar mai suna Henry Kemende ne bayan zargin wasu 'yan bindiga da ba a kai ga tantance su ba da halaka shi a ranar Talata.
Shi dai marigayin dan majalisar na Kamaru, dan jam'iyyar nan ta Social Democratic Front ne da ke hamayya.
Mataimakin shugaban jam'iyyar SDF, Joshua Osih, ya ce sun karbi gawar dan majalisar dauke da harbin bindiga a jiki.
Ya zuwa yanzu babu wani ko wasu da suka dauki alhakin kisan dan majalisar na Kamaru.