An kammala taron kan sauyin yanayi a birnin Vienna | Labarai | DW | 01.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron kan sauyin yanayi a birnin Vienna

Wakilai a gun wani babban taron kasa da kasa kan sauyin yanayi sun amince da wata yarjejeniya da ba ta wajaba ba don rage hayaki mai gurbata yanayi. Bayan sun shafe tsawon mako guda suna tattaunawa a birnin Vienna mahalarta taron sun amince kan muhimmancin rage fid da wannan hayaki da misalin kashe 25 zuwa 45 cikin 100 kafin shekara ta 2020 idan aka kwatanta da yawansa a shekarar 1999 musamman daga bangaren kasashe masu ci-gaban masana´antu. An gudanar da taron ne wanda sashen yaki da sauyin yanayi na MDD ya shirya don sharen fagen taron kolin kan yanayi da wanda zai gudana a tsibirin Bali na kasar Indonesia a cikin watan desamba. Manufar taron na Bali ita ce cimma sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa wadda zata maye gurbin yarjejeniyar birnin Kyoto akan rage fid da gurbataccen hayaki. A shekara ta 2012 yarjejeniyar ta Kyoto take kare aiki.