An kama wani da hadin baki a harin Berlin | Labarai | DW | 28.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wani da hadin baki a harin Berlin

'Yan sandan Jamus sun kama wani dan Tunisiya wanda ake zargi an hada baki da shi wajen kai harin kasuwar Kirsimeti a Berlin.

Masu gabatar da kara na Jamus sun ce sun kama wani dan Tunisiya wanda ake kyautata tsammanin da shi aka kai harin kasuwar KIrsimeti a Berlin a makon da ya wuce. Masu gabatar da karar na tarayya suka ce mutumin mai shekaru 40 an kama shi ne bayan da aka gudanar da bincike a gidansa da kuma wurin kasuwancinsa. Sun kara da cewa an sami lambarsa a wayar Anis Amri wanda ake kyautata zaton shine ya tuka babbar motar da aka kai harin da ita a ranar 19 ga watan Disamba.