An kama sojojin da suka kashe mata a Kamaru
July 19, 2018Talla
Rahotannin da ke fitowa daga kasar Kamaru na cewa an cafke wasu sojoji hudu da aka yi zarginsu da kashe wasu mata biyu goye da 'ya'yansu biyu a yankin arewa mai nisa.
Wata majiyar tsaro ce ta tabbatar da wannan labarin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya labarta.
Wani faifan bidiyo da ya fito a makon jiya, da kuma daruruwan dubban mutane suka yi ta gani, ya matukar tayar da hankalin al'umar duniya, inda aka yi ta kiraye-kirayen a dauki mataki.
Tunda fari dai kakakin gwamnatin kasar ta Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya musanta sahihancin labarin, koda ya ke ya amince cewar za a gudanar da bincike.
Wata majiyar ma ta tsaro, ta ce an ma aika uku daga cikin sojojin zuwa Yaounde babban birnin kasar, yayin da daya ke a garin Maroua.