An kakkabe mayakan IS daga Aleppo | Labarai | DW | 30.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kakkabe mayakan IS daga Aleppo

Rahotannin da ke fitowa daga Aleppon kasar Syria, na cewa dakarun gwamnatin kasar sun kakkabe mayakan IS da ke yankin sakamakon janyewar da suka yi a ilahirin yankunan da ke kewayen lardin.

Shugaban kungiyar kare hakki ta Syrian Observatory for Human Rights, Rami Abdl Rahman, ya ce tuni mayakan na IS suka janye daga akalla garuruwa 17. Wasu shaidu sun ce lamari ya soma rikice wa mayakan na IS ne a daren da ya gabata, lokacin da dakarun Syria suka karbe wata hanyar da ta hada yankin Aleppo da Raqqa da ma sauran wasu wuraren.

Wata rundunar soji da ke wani kauyen Aleppo, ta tabbatar da bayanan kungiyar dangane da karbe wadannan garuruwa daga mayakan na tarzoma. Shekaru biyu kenan da sojoji ke ta bata kashi da mayakan na IS a musamman yankin na Aleppo.