1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kai wani sabon harin rokoki a Kabul

August 30, 2021

An kai wani sabon harin rokoki a kusa da filin saukar jirage na Hamid Karzai da ke a birnin Kabul na Afghanistan, a daidai lokacin da Amirka ke kan kokarin janyewa daga kasar.

https://p.dw.com/p/3zf7u
Afghanistan Kabul | Zerstörtes Auto nach Rekatenangriff
Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

Fadar White House ta Amirka ta tabbatar da harin da aka kai a wurin da aka kira Salim Karwan. An kuma ji karar harbe-harbe lokacin da rokokin ke sauka.

A gefe gudu kuwa harin nan da Amirka ta kai a kan kusoshin mayakan IS a Afghanistan a ranar Lahadi, ya yi sanadiyyar wasu fararen hula.

Sojojin Amirka da suka tabbatar da hakan, sun ce daga cikin wadanda abin ya shafa dai har da wasu kananan yara hudu a kusa da filin jirgin saman na Kabul.

Shaidu ma sun ce mutane shida suka mutu a harin na jiya da Amirka ta yi amfani da jirgi marar matuki, yayin da karin mutane da yawa suka kuma jikkata.