An kai hari kan sojojin Najeriya a Mali | Labarai | DW | 05.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan sojojin Najeriya a Mali

Ba a bayyana yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba a harin na kusa da Timbuktu. Amma dakarun kasa da kasa sun yi wa mayakan kofar rago a garin na Arewacin Mali.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kusa da Timbuktu a Arewacin Mali. Kakakin rundunar MINUSMA Olivier Salgado ya bayyana cewar 'yan bindigan sun fara tarwatsa motsa da ke ciki da bama-bamai kafin su far wa sojojin Najeriya da ke jibge a wannan sansani.

Dakarun Mali tare da hadin gwiwar sojojin kawance sun yi wa 'yan bindigan kawanya, inda rahotanni suka nunar da cewar ana ci gaba da bata kashi tsakanin bangarorin biyu. Ba a dai bayyana yawan mutane da suka rasa rayukansu a wannan harin ba. Amma shaidu sun sanar da cewar sun ga gawarwarki da dama a wajen wannan sansani.

Sojojin Jamus na daga cikin wadanda suke bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Arewacin Mali, inda gwamnatin wannan kasa ke niyar turawa da sojoji 650 a Mali.