An kai hari cikin wani masallaci a Pakistan | Labarai | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari cikin wani masallaci a Pakistan

Wasu 'yan bindiga, sun kai hari a wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Peshawar na kasar Pakistan a wannan Jumma'a, inda harin ya hallaka mutane da dama tare da jikkata wasu.

Mutane 19 sun hallaka a wannan Jumma'a sakamakon harin da aka kai a wani masallacin 'yan Shi'a a birnin Peshawar da ke arewacin wannan kasa a cewar wata majiya ta jami'an kiwon lafiya. Wasu mutane ne dai dauke da makammai suka buda wuta yayin da ake sallar Jumma'a, sannan daga bisani wasu ababe guda uku suka fashe a cikin masallacin a cewa Jami'an tsaro.

Tuni dai jami'an tsaro suka dukufa wajan neman 'yan ta'addan a cewar shugaban 'yan sandar yankin na Peshawar. Da ma dai a watan Janairu da ya gabata wani harin da wata kungiyar 'yan Sunna ta dauki alhakinsa, ya yi sanadiyar rasuwar mutane 50 cikin masallacin 'yan Shi'a a birnin Shikarpur.