An kai hari a jihar Bauchi | Labarai | DW | 29.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a jihar Bauchi

'Yan bindiga sun kai hari a kauyen Bauchi na Najeriya yayin da ake ci gaba da zabe a kasar.

Rahotannin da ke fitowa daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa dakarun kasar sun yi dauki-ba-dadi da wasu mayakan Boko Haram a kauyen Dungulbe da ke cikin jihar Bauchi, da safiyar yau Lahadi.

Shaidu sun ce mayakan na Boko Haram sun shiga kauyen ne da misalin karfe goma na safiya, cikin motocin a-kori-kura 20 dauke da muggan makamai, sai dai sojojin sun far musu ta sama da kuma kasa.

Wani jami'in soji da ya zanta da kamfanin labaran Faransa AFP, ya yi ikirarin cewa sojin sun nakasa mayakan na Boko Haram, kuma ma ana ci gaba da barin harsasai.

Kamar yadda shima wani da ya tsere daga kauyen na Dungulbe, Mudassir Hambali ya shaidar, mayakan na Boko Haram na kokarin kafa sansani a kauyen ne, a cewarsu.