An haramta wa Rasha halartar kakar wasannin nakasassu | Labarai | DW | 29.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An haramta wa Rasha halartar kakar wasannin nakasassu

Rasha ba za ta halarci kakar gasar wasannin nakasassu ta Paralympics da za a gudanar a kasar Koriya ta Kudu a watan Maris na wannan shekara ba sakamakon samun 'yan wasan kasar da shan miyagun kwayoyi a baya.

Wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da irin wadannan wasanni na nakasassu ba tare da kasar ta Rasha ba. A shekara ta 2016 ma kasar ba ta samu shiga irin wadannan wasannin da aka gudanar a birnin Rio de Janeiro ba sakamakon irin wannan zargi na samun wasanta da amfani da kwaoyin kara kuzari.

Da yake karin haske a kan wannan batu shugaban kwamitin wasannin nakassun ta duniya Andrew Parsons ya bayyana cewar akwai yiwuwar ba wasu 'yan kalilan daga cikin 'yan wasannin na Rasha damar shiga gasar bayan an yi musu gwaje-gwaje tare da halartar horo a kan yaki da shan kwayoyi.