An hallaka mayakan IS da dama | Labarai | DW | 16.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka mayakan IS da dama

Hare-haren da sojin Amirka ke jagoranta don kawar da kungiyar nan ta IS sun hallaka daruruwan 'yan kungiyar kusa da Kobani daura da kan iyakar Siriya da Turkiyya.

Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon da ta tabbatar da wannan labarin ta ce dakarun kawacen da Amirkan ke jagorantan sun samu nasarar hallaka 'yan kungiyar ta IS ne a hare-hare kimanin 40 da suka kai ta sama a cikin kwanakin biyun da suka gabata.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan shi ne ta'adi mafi muni da aka yi wa 'yan kungiyar ta IS a baya-bayan nan. An dai alakanta wannan nasarar da dakarun kawance suka samu da irin bayanan sirrin da sojin Kurdawa suka baiwa sojin Amirka.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amirkan John Kirby ya ce duk da irin yunkurin 'yan IS na karbe iko da Kobani, har yanzu dai garin na karkashin ikon dakarun Kurdawa.