1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawar Janar Alkali

Abdullahi Maidawa Kurgwi MA
October 31, 2018

Hukumomi a Najeriya sun ce an gano gawar Janar din ne a wata rijiya cikin gundumar Shen ta karamar hukumar Jos ta Kudu.

https://p.dw.com/p/37Tej
Nigeria Bodentruppen
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewar ta gano gawar Manjo Janar Idris Alkali ne, babban hafsan da ya bace a jihar Filato da ke a arewa maso tsakiyar kasar.

Rundunar ta ce an gano gawar Janar Alkalin ne a wata rijiyar da ke kauyen Guchwet cikin gundumar Shen ta karamar hukumar Jos ta kudu.

A wata sanarwa ga manema labarai a birnin na Jos a wannan Laraba, jagoran masu bincike kan bacewar babban hafsan, Birgediya Janar Umaru Mohammed, ya ce rundunar sojin za ta shirya wa marigayi Alkali kasaitaccen bizina irin ta girmamawar soji.

Wakilinmu na jihar ta Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya ruwaito cewar jama'a na ta bayyana ra'ayoyi tun bayan bacewar Manjo Janar Alkali, a ranar 3 ga watan jiya na Satumba, bayan ya baro Abuja kan hanyarsa ta zuwa Bauchi.