An fara samun ci gaba kan Ebola a Laberiya | Labarai | DW | 30.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara samun ci gaba kan Ebola a Laberiya

Hukumomin kasar Laberiya sun sanar da batun dage killacewar da suka ayyana kan unguwar West Point da ke Monrovia sakamakon ci gaban da aka samu

A wata sanarwa ce da fadar shugabar kasar ta fitar a jiya Juma'a(29.08.2014). Wannan mataki dai ya biyo bayan bukatar da Ministan kiwon lafiyar kasar ya shigar ta neman a dage matakin killacewar dangane da ci gaban da aka samu na raguwar yaduwar cutar ta Ebola a wannan unguwa sakamakon hadin kan da al'umma ta bayar tun bayan da aka killace ta a cewar Ministan sadarwar kasar Lewis Brown.

Ministan ya kara da cewa, al'ummar wannan unguwa dai ta nuna matukar fahimta kan wannan lamari, tare da ba da cikeken hadin kanta wajen yaki da yaduwar cutar ta hanyar kula da sa'ido, da kuma fadakarwa kan hanyoyin gujewa kamuwa da cutar. Cutar ta Ebola dai da kawo yanzu ta yi sanadiyar rasuwar fiye da mutane 1500 a yammacin Afirka, ta bulla a karon farko a kasar Senegal a cewar hukumomin kiwon lafiyar wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo