An dakatar da aikin ceto dalibai a Lagos | Labarai | DW | 14.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakatar da aikin ceto dalibai a Lagos

Kwana guda bayan rushewar wani gini a Lagos da ke kudancin Najeriya, hukumomi sun dauki matakin dakatar da bincike duk da nasarar ceto mutane 37 da suka yi yayin da akalla takwas suka rasa rayukansu.

Wani jami'in gwamnati Najeriya ya ce an dakatar da aikin ceto mutanen da gini ya binne bayan rushewar wata makarantar a Legos da ke yankin Kudu maso yammacin kasar. Ibrahim Farinloye na Hukumar agaji gaggawa ta kasa ya bayyana wa kanfanin dillancin labarai na Associated Press cewa ma'aikatan ceto ba sa sa ran ganin wasu karin gawarwaki bayan da suka cimma tubalin ginin.

Sai babban jami'in ya ki bayyana adadin yaran da aka ceto da wadanda suka rasa rayukansu. Amma jami'ai sun bayyana a jiya laraba cewa mutane takwas ne sukan mutu yayin da aka yi nasarar ceto 37.