An dage fadar sakamakon zaben shugaban kasar Mali | Labarai | DW | 01.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage fadar sakamakon zaben shugaban kasar Mali

Mahukuntan Mali sun ce sun dage bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.

A man casts his vote during Mali's presidential election in Timbuktu, Mali, July 28, 2013. REUTERS/Joe Penney (MALI - Tags: ELECTIONS POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)

Mali Wahlen Wähler Urne 28.07.2013

Ofishin shugaban kasar ne ya bada wannan sanarwar dazun nan, sai dai sanarwar ba ta yi wani cikakken bayani game da dalilin da ya sanya ta dage bayyana sakamakon ba, amma wani jami'i da ya zabi a sakaya sunansa ya ce kidayar kuri'un da ba a kammala ba ce ta sanya dage bayyana sakamakon.

A ranar Talatar da ta gabata dai ofishin ministan cikin gidan Mali din ya shaida cewar tsohon firaministan kasar Ibrahim Boubakar Keita ne kan gaba da rinjayen gaske amma kuma wasu daga cikin 'yan takara a zaben sun sanya kafa sun shure wannan kalamai da ministan ya yi domin a cewarsu ya gaza bada wata cikakkiyar hujja musamman ma ta alkaluma da za ta tabbatar da hakan.

Zaben na Lahadi dai shi ne zabe na farko da kasar ta shirya tun bayan da aka hambarar da gwamnatin farar hular kasar a farkon shekarar da ta gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal