1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Turkiyya ta ci gaba da tsare sojojin Girka biyu

Suleiman Babayo MAB
July 17, 2018

Wata kotu a kasar Turkiyya ta ba da umurnin ci gaba da tsare sojojin Girka biyu wadanda ake tuhumar leken asiri.

https://p.dw.com/p/31cUV
Edirne Türkei 2 griechische Soldaten inhaftiert
Hoto: Imago/Depo Photos/DHA

Wata kotun Turkiyya ta yanke hukuncin ci gaba da tsare sojojin Girka biyu bisa tuhuma kan leken asiri tun watan Maris. A wannan Talata kotun ta yi watsi da bukatar da lauyan sojojin ya gabatar matata kan neman bayar da belin sojojin biyu.

Kan wannan batu Firaminista Alexis Tsipras na Girka ya gana da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a gefen taron kungiyar tsaro ta NATO-OTAN a birnin Brussels na Beljiyam a makon jiya.