An ceto mata daga hannun Boko Haram | Labarai | DW | 29.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto mata daga hannun Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kubutar da mata 293 a wata fafatawa da suka yi da 'yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

A wani sako da ya fidda ta shafin twitter, kakakin rundunar sojin kasar Chris Olukolade ya ce daga cikin wannan adadi da aka kubutar 200 'yan mata ne sai dai ba a hakikance ko su ne 'yan matan nan na Chibok da aka sace a bara ba.

Rundunar sojin ta Najeriya ta ce yanzu haka ta na yi musu tambayoyi don tantance daga inda suka fito kafin daga bisani ta yi cikakken bayani dangane da hakan.

Kungiyar Boko Haram da ta shafe shekaru shidda ta na tada kayar baya a Najeriya ta hallaka dubban mutane da kuma sace daruruwan yara maza da mata.