Najeriya: 'Yan matan da aka sace a Neja sun tsere
November 23, 2025
Jami'an tsaron Najeriya sun ceto wasu mutane 38 mabiya addinin Kirista da aka yi garkuwa da su a wani harin na ranar Talatar da tagabata, a daidai lokacin da suke tsaka da ibada a kauyen Eruku na jihar Kwara.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanar a wani sakon da ya fitar a ranar Lahadi, yana mai cewa tare "da taimakon jami'an tsaronmu, daukacin masu ibadar da aka sace daga cocin Eruku na jihar Kwara sun kubuta". Duk da yake shugaban bai yi wani karin haske ba.
'Yan matan da ake yi garkuwa da su sun kubuta
Dalibai 50 daga cikin fiye da 300 da aka sace a makarantar nan ta Katolika da ke jihar Neja sun tsere daga hannun masu garkuwa da su, in ji kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya, amma kungiyar, ba ta yi wani karin haske kan ragowar daliban ba da malamansu 12 da hadarin ya rutsa da su ba.
Wane hali iyayen dalibai ke ciki a Kebbi?
Wasu masu dauke da makamai da har yanzu ba a tabbatar da ko su wane ne ba, suka kai hari a sanyin safiyar ranar Juma’a a makarantar St. Mary's Catholic School da ke jihar Neja, tare da sace daliban fiye da 300, satar da ke zaman irinta mafi muni a tarihin kasar, tun bayan sace 'yan matan Chibok shekaru 10 da suka gabata.
Ba wata kungiya da ta yi ikrarin kai harin tare da sace 'yan mata
Har yanzu ba wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai harin na jihar Neja, ko kuwa harin Maga na jihar Kebbi a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Jagoran mabiya darikar Katolika Léon na 14 ya yi kira da a ceto daliban da aka yi garkuwa da su, tare da nuna kaduwarsa game da sace-sacen malaman addnini da dalibai a kasashen Najeriya da Kamaru.
'Yan bindiga sun sace 'yan makaranta 25 a Najeriya
Shugaban Amurka Donalnd Trump, da ya yi barazanar kai wa 'yan ta'adda hari don ceto Kiristocin Najeriya, ya bayyana abin da ke faruwa a Najeriya amatsayin abin kunya.