An ceto bakin-haure a tekun Libiya | Labarai | DW | 12.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto bakin-haure a tekun Libiya

Masu gadin tekun Libiya sun kama jirgin ruwa dauke da bakin-haure fiye da 20


Masu gadin gabar tekun Libiya sun bayyana kama wani jirgin ruwa dauke da bakin-haure fiye da 20 masu neman tsallaka teku domin shiga kasashen Turai. Kofofin yada labaran kasar ta Libiya sun ce bakin-haure sun fito daga kasashen Masar, da Sudan, gami da Libiya.

A cikin wata sanarwa hukumomin sun bayyana mika mutane ga masu aikin jinkai gami da taimakon lafiya, inda aka kai su wani sasansanin 'yan gudun hijira.