An ceto bakin haure a Libiya | Labarai | DW | 24.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto bakin haure a Libiya

Sojojin ruwa a Libiya sun ce sun ceto wasu jiragen ruwa uku shake da bakin haure a tekun Bahar Rum, wadanda ke kokarin shiga kasashen Turai.

Jiragen na ruwa na dauke ne da mutane akalla 290 da suka fito galibi daga kasashen Afirka da kuma wasu larabawa da ma wasu 'yan kasar Bangaladesh.

Ko a ranar Alhamis ma masu gadin gabar ruwan Libiyar, sun ce an sami wani jirgin ruwan da ya fuskanci matsalar, sakamakon yadda ruwa ke ta shiga cikinsa, yana kuma dauke da bakin haure 87.

Ita ma wata kungiyar kasar Jamus da ke sa ido kan tekun, ta je jirginta na sama ya ceto wasu bakin na haure a Alhamis din.