An cafke ′yan Kungiyar Al-Ka′ida a Jordan | Siyasa | DW | 27.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An cafke 'yan Kungiyar Al-Ka'ida a Jordan

Jami'an tsaron kasar Jordan sun fallasa wata makarkashiya ta harin ta'addancin da aka yi niyyar kaiwa a Amman fadar mulkin kasar

Dakarun kundumbala na kasar Jordan lokacin da suka kai samame a kan 'yan ta'adda

Dakarun kundumbala na kasar Jordan lokacin da suka kai samame a kan 'yan ta'adda

Dakarun kundumbala na kasar Jordan sun kai samame a wani gida mai dufun gaske, inda suka samu nasarar karya alkadarin ‚yan ta’addan bayan ‚yar musayar wuta da kuma wata hayaniyar da aka rika ji a hoton telebijin da aka dauka. Wannan hoton dai ya kunshi cikakkun bayanai ne a game da matakin cafke ‚yan ta’addan a birnin Amman, fadar mulkin kasar Jordan. A baya ga haka, kamar yadda rahotanni masu nasaba da mahukuntan kasar suka nunar an halaka wasu ‚yan ta’addan su hudu a wasu matakan samame dabam-dabam da aka dauka. To sai dai kuma babban abin da ya fi daukar hankalin jama’a fiye da hotunan na telebijin shi ne sanarwar da aka ji daga bakin wani jami’in tsaron dake cewar wannan makarkashiyar ta ta’addancin da aka shirya tana da nufin halaka mutane akalla dubu 80 da kuma raunana wasu dubu 160 a birnin Amman ta kai musu hari da makaman guba. An kwace tan ashirin na abubuwa masu bindiga daga hannun ‚yan ta’addan da kuma wasu gangunan roba dake kunshe da magunguna masu guba. Harin dai an shirya kaiwa ne akan ofishin hukumar leken asirin kasar Jordan da fadar P/M kasar da kuma ofishin jakadancin Amurka. Daya abin da ya dauki hankalin jama’a kuma shi ne finafinan video da aka nunar inda ‚yan ta’addan ke hakikancewa da laifin da ake zarginsu da shi. Azmi El-Jayusi dan kasar Jordan shi ne madugun ‚yan ta’addan, wadanda suka ce wai ya samu umarni da kuma gudummawar dala dubu 170 ne daga Abu Musab El Zaqawi, shi ma dai dan kasar Jordan ne dake da hulda ta kut-da-kut da shugaban kungiyar Al-Ka-ida Usama Bin Laden, wanda kuma Amurka ke ikirarin cewar shi ne uammal’aba’isin wasu daga cikin hare-haren da ake fama da su a Iraki. A lokacin da yake bayani El-Jayusi karawa yayi da cewar:

Bayan da na isa Iraki daga Afghanistan na hadu da Abu Musab Azzarqawi a can, wanda ya umarce ni da in zarce zuwa Jordan domin shirya wasu matakai da za a dauka bisa manufa. Kazalika shi ne ya taimaka na samu sukunin shiga kasar Jordan ba tare da wata tangarda ba.

Majiyoyi masu nasaba da mahukuntan Jordan sun ce su kansu tuhumammun da kuma lauyoyinsu ne suka amince da a dauki wadannan fina-finai na video. Mahukuntan suka ce fallasa wannan makarkashiya da aka yi abu ne dake tabbatar da wanzuwar 'yan kungiyar al-Ka’ida a wannan kasa, wadanda tun da farkon fari aka yi damarar tinkarasu. Ita dai kasar Jordan tana da dangantaka ta kut-da-kut da kasar Amurka duk da cewar Sarki Abdallah na biyu yana Allah Waddai da yakin Iraki.