An cafke mutane biyar kan harin Berlin
March 29, 2018Talla
Anis Amri wanda Jamus ta hanawa izinin samun mafakar siyasa, ya afkawa kasuwar gargajiya kirsimeti a birnin Berlin da wata katuwar satacciyar mota, inda ya kashe mutane 12 tare da raunata wasu 100.
Mayakan IS sun dauki alhalin wannan harin na 19 ga watan Disamban 2016, wanda ke zama mafi munin harin da ya taba ritsawa da Jamus. Bayan kwanaki hudu da kai wannan harin ne 'yan sandan Italiyan suka harbe Amri a kusa da birnin Milan.
Ana zargin mutane biyar da aka capke a yau Alhamis din da laifin ta'addancin kasa da kasa, daura da samarwa da 'yan cirani jabun takardu, a cewar kafofin yada labarun Italiyan.