An cafke masu zanga-zanga a Masar | Labarai | DW | 21.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke masu zanga-zanga a Masar

'Yan sanda a Masar sun cafke sama da 'yan kasar 70 daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar neman murabus din shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi.

Daruruwan Misrawan ne dai suka yi wa manyan titunan Alkahira babban birnin kasar tsinke da yammacin jiya Juma'a, inda suka yi ta kiraye-kirayen Shuagaba al-Sisi da ya sauka daga mukaminsa.

Rahotannin da ke fitowa daga kasar na cewa 'yan sanda musamman na ciki, na ci gaba da tsananta sintiri na sirri don ci gaba da zakulo wadanda ake zargi da kasancewa kusoshi da suka hada gangamin.

Haka nan ma wasu zaratan jami'an tsaro sun mamaye dandalin 'yanci na Tahrir, dandalin da a nan ne 'yan kasar ta Masar suka ga bayan mulkin marigayi tsohon Shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011.

Masar din dai ta haramta duk wata zanga-zanga a wata dokar da ta samar a shekarar 2013.