1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An bukaci gwamnati ta saki Zakzaky

January 3, 2020

 A Najeriya wani lauya mai zaman kansa a kasar ya nemi gwamnatin kasar da ta saki Sheik Ibrahim Alzakzaky jagoran mabiya mazahabin Shi'a a Najeriya domin tabbatar da bin doka da oda

https://p.dw.com/p/3Vh8h
Nigeria Anhänger von Schiiten-Führer Ibrahim Zakzaky
Hoto: AFP/S. Adelakun

 A Najeriya wani lauya mai zaman kansa a kasar ya nemi gwamnatin kasar da ta saki Sheik Ibrahim Alzakzaky jagoran mabiya mazahabin Shi'a a Najeriya domin tabbatar da bin doka da oda bayan da wasu kotunan kasar suka ba da umurnin sakinsa. Sheik Alzakzaky dai ya share shekaru a hannun jami'an tsaron kasar ta Najeriya wadanda ke ci gaba da tsare shi duk da umurnin sakin nasa daga kotu.

A cikin wata wasikar da ke zaman ta ba-zata, lauyan na Zakzaky kuma dan karajin kare 'yanci cikin kasar Femi Falana, ya nemi mahukuntan Tarrayar Najeriyar da su saki shugaban kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi da nufin tabbatar da bin dokar da take ikirari.
Wasikar da ta zo mako guda kacal bayan sakin Sambo Dasuki da ma Omoyele Sowore ta ce sakin na Zakzaky zai tabbatar da cika burinta na sabon babin bin dokoki da ma umarnin kotu cikin kasar kamar yadda shugaban ya shaida wa al'ummar Tarrayar Najeriyar a jawabinsa na  sabuwa ta shekara. Lauyan dai ya ce wata Kotun tarrayar a Abuja ta nemi ba da belin na Zakzaky a watan Disamban shekara ta 2016, kafin mahukunta na kasar su sa kafa su shure bukatar da ta kalli jagoran yan shi'an da ya share kusan shekaru hudu yana hannu na jami'an tsaron Tarrayar Najeriyar.

Karikatur Boko Haram
Hoto: DW/Baba

To sai dai kuma kasa da 'yan awoyi da wasikar da lauyan ya mika ga ministan shari'ar Tarrayar Najeriyar dai,  gwamnatin ta ce matakin lauyan bai wuci kokarin siyasa da batun shari'a ba.
Malam Garba Shehu dai na zaman kakaki na gwamnatin da kuma ya ce babu falanan na kokari na siyasa da makoma ta Zakzaky da ke shari'a da jihar Kaduna a halin yanzu.

Zaman lafiya na dukkan al'umma ko kuma 'yancin kowa cikin kasa, Zakzaky dai na zaman daya a cikin kalilan na wadanda ake yi wa kallo a matsayin fursunoni na siyasar Tarrayar Najeriyar da ke daukar hankali. To sai dai kuma a fadar barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa, gwamnatin tarrayar na iya karbe shari'ar duk da kasancewarta a hannun gwamnatin jihar.

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Dama dai wani rikici ne a tsakanin babban hafsan sojan kasar ta Najeriyar da magoya bayan malamin 'yan shi'an ya rikide ya zuwa fito na fito da kame da dama a tsakanin bangaren 'yan shi'an. Kuma a fadar Isa Sunusi da ke zaman kakakin kungiyar Amnesty International mai fafuktukar kare hakkin bil'adama, tabbatar da adalci kan daukacin kasar ne ke iya kaiwa ya zuwa bude sabon babi ga rayuwa da ma ci-gaban kasar da ke neman sauyawa. 

 A cikin wata wasikar da ya aike wa daukacin al'ummar Tarrayar Najeriyar da nufin bude sabuwar shekara, shugaba kasar Muhammad Buhari dai ya ce gwamnatinsa za ta kasance mai bin doka da tabbatar da 'yancin kowa a kasar.