An bude taron kolin kasashen nahiyar Amirka a Mar Del Plata a Argentina | Labarai | DW | 05.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kolin kasashen nahiyar Amirka a Mar Del Plata a Argentina

A wani yanayi na tashe tashen hankula da jerin zanga-zangar kin lamirin shugaban Amirka GWB, an bude taron kolin kasashen nahiyar Amirka karo na 4 a birnin Mar del Plata na kasar Argentina. Kimanin masu zanga-zanga 300 sun cunnawa ginin wani bankin Amirka da kuma kantuna da dama wuta sannan kuma sun yi ta jifar ´yan sanda da duwatsu. Tun gabanin fara taron kolin dubun dubatan mutane a fadin kasar ta Argentina sun gudanar da zanga-zangar lumana don yin Alah wadai da shirin kafa wani yankin ciniki maras shinge a fadin nahiyar Amirka kamar yadda kasar Amirka ke bukata. Wasu kasashen yankin kamar Argentina da Brazil da Venezuella na nuna adawa da kafa wannan yanki na ciniki musamman dangane da kayyade yawan kayan amfani gona da ake shigar da su Amirka da gwamnatin birnin Washngton ta yi. Saboda haka ba´a tsammanin cimma wata yarjejeniya bisa wannan manufa a taron na birnin Mar del Plata. Gwamnatocin kasashe 34 na yankin Amirka ke halartar taron.