1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

An bankado malamai na ci da gumin gwamnati a Sokoto

May 23, 2024

Kwamitin da aka kafa domin zagaya makarantun Sakandare da Firamari a jihar Sakkwato ya gano galibin malaman makarantun ba sa zuwa makarantun gwamnati duk da yake suna karbar albashi.

https://p.dw.com/p/4gCJk
Daliban makarantar boko a ajin daukar darasi a Najeriya
Daliban makarantar boko a ajin daukar darasi a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kwamitin ya ga halin da wata makaranta Sakandare ta ke ciki da malamai kusan 30 ne kawai ke zuwa koyar da darasi a makarantar daga cikin malamai 98 da makarantar take da su, kana kwamitin ya hakikance galibin malaman makarantar da ba sa zuwa zuwa karantarwa matan manya ne da kuma 'ya'yan masu fada aji a Najeriya.

Wannan lamari ya sanya ilimin makarantun Firamari da Sakandare da ke karkashin kulawar gwamnati fuskantar koma baya, sai dai kwamitin ya ce shugabannin makarantun sun tabbatar masa da cewa sun sha kai korafi amma saboda galihu da ke ga wasu malaman ba bu wani mataki da aka dauka akai.

Shugabannin kwamitin sun nuna fargaba kan irin yadda makomar ilimin arewacin Najeriya za ta kasance idan aka yi la'kari da halin da rikon sakainar kashi da wasu malamai ke yi wa harkar  Ilimi a arewacin Najeriya.