An ba da lambar yabo ta Nobel | Labarai | DW | 10.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ba da lambar yabo ta Nobel

Kwamitin da ke kula da bada lambar yabo ta zaman lafiya ta ya bayyana Malala Yousafzai da kuma Kailash Satyarth da cewar su ne suka lashe kyautar ta shekara ta 2014.

Kwamitin ya bayyana Nalala Yousafzai 'yar Pakistan ɗin nan, wadda 'yan Taliban suka yi yununƙuri hallakata a shekaun 2012 saboda fafutkar da ta ke yi na samar da ilimi ga yara.Da kuma wani dan ƙasar Indiya mai fafutkar samar da ilimi shi ma da kuma yaƙi da cin zarafin yara Kailash Satyarth.

Kyautar wacce ta ƙunshi kuɗaɗe Euro dubu ɗari tara za a ba da ta nan gaba a ranar goma ga watan Disamba da ke tafe.