1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta sake bijire wa kokarin kawo karshen yaki a Gaza

September 19, 2025

Amurka ta sake amfani da ikonta na hawa kan kujerar na ki a kan wani kudurin da ya bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a game da dakatarda yaki a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/50laG
Kwamitin Sulhu na MDD | Kuri’ar da aka kada kan tsagaita wuta a Gaza da taimakon jinkai
Kwamitin Sulhu na MDD | Kuri’ar da aka kada kan tsagaita wuta a Gaza Hoto: Michael M. Santiago/Getty Images

Kasar ta Amurka ce dai kadai ta kada kuri'ar adawa, yayin da sauran kasashe 14 ciki har da Rasha da China da Burtaniya da Faransa da sauran mambobin wucin gadi 10 suka goyi bayan kudurin.

Kudurin ya nuna damuwa matuka kan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da kira ga gwamnatin Isra'ila ta gaggauta janye duk wani hani ga shigar da agajin jinkai zuwa Gaza.

Wannan dai shi ne taro na 10,000 na kwamitin sulhun tun bayan kafa ta shekaru 80 da suka gabata, a cewar Majalisar Dinkin Duniya,.

Wakiliyar Amurka, Morgan Ortagus, ta kare wannan mataki na adawa da hujjar cewa kudurin da ta kira “maras karbuwa” da ke mara wa kungiyar Hamas baya.