1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta dakatar da bai wa Isra'ila tallafin makamai

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 8, 2024

Matakin na White House ya zo ne makon da ya gabata, lokacin da Isra'ilan ta gaza yin cikakken bayanin da zai gamsar da Amurka

https://p.dw.com/p/4fbth
Hoto: Chris Kleponis/ZUMA Wire/Imago Images

Amurka ta dakatar da bai wa Isra'ila tarin makamai da suka hada da bama-bamai, sakamakon fargabar far wa birnin Rafah da ke Kudancin Gaza da Amurkan ta yi, a karon farko kenan da shugaba Joe Biden ya janye tallafin tsaro ga Isra'ila.

Karin bayani:Biden ya caccaki Isra'ila kan salon yakinta a Gaza

Matakin na White House ya zo ne a makon da ya gabata, lokacin da Isra'ilan ta gaza yin cikakken bayanin da zai gamsar da Amurka kan batun, in ji wani babban jami'in Amurka.

Karin bayani:Shugaba Joe Biden na Amurka da Donald Trump sun caccaki juna a yakin neman zabe

Shugaba Joe Biden na fuskantar matsin lamba ta cikin gida, inda dubban daliban jami'o'in Amurka ke ci gaba da zanga-zangar adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, inda suke ci gaba da yin arangama da 'yan sanda.

A gefe guda kuma Mr Biden na fuskantar karin matsin lamba daga tsohon shugaban kasar Donald Trump, a daidai lokacin babban zaben kasar na watan Nuwamba ke karatowa.