1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka na shirin janye sojojinta daga Siriya

February 19, 2026

Jaridun Amurka sun ruwaito cewa Washington na shirin janye daukacin sojojinta 1,000 da ta jibge a Siriya nan da watanni biyu masu zuwa saboda kasar ta fara hawa kan saiti.

https://p.dw.com/p/590rD
Sojojin Amurka na sintiri a Siriya
Sojojin Amurka na sintiri a SiriyaHoto: Baderkhan Ahmad/AP/picture alliance

Jaridar Wall Street ta Amurka ta ruwaito cewa Washington za ta kawo karshen zaman dakarun sojinta a Siriya bayan da fadar mulki ta Damascus ta fadada ikonta a yankunan kasar.

Kazalika matakin na da nasaba da yarjejeniyar da gwamnatin Siriya ta rattaba a karshen watan Janairu na wannan shekara wata ta jibanci shigar da mayakan Kurdawa na SDF cikin aikin soji bayan rawar da suka taka wajen kifar da gwamnatin Al-assad.

Ahmed al-Sharaa ya gana da Donald Trump

A ranar Lahadi da ta gabata an jiyo sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio na yabawa da alkibtar da Siriya ta dosa a halin yanzu, duk da yanani na wahala da ya ce kasar ta fuskata a baya.

Turkiyya na kokarin kaucewa rikici tsakanin Iran da Amurka

A gefe guda kuma gidajen talabijin na CNN da CBS sun ba da rahoton cewa sojojin Amurka a shirye suke su kaddamar wa Iran hare-hare a karshen wannan mako, ko da yake sun ce har yanzu Donald Trump bai yanke shawara karshe ba.