Amnesty ta kalubalanci kame mata a Imo
August 24, 2018Wani alkali a birnin Oweri na jihar Imo, ya nemi ci gaba da tsare matan da aka kame a lokacin zanga-zanagar har zuwa watan Satumba mai zuwa. Sai dai kungiyar Amnesty International na ganin matakin a matsayin wuce gona da iri kamar yadda kakin kungiyar a Najeriya Isa Sunusi ya sheda wa DW: "Kundin tsarin mulki ya ba wa kowa 'yancin fadin albarkacin bakinsa, muna kira da a gaggauta sako su, tun da dai ba su tayar da hankalin kowa ba."
Kame sama da mata 100 da aka yi, na zuwa ne kasa da 'yan sa'o'i da wani zaben kananan hukumomi a jihar Imo, wannan ya sa ake danganta zanga-zangar da siyasa. Kungiyar IPOB ta jima tana fafutukar neman rajin ballewa daga Najerya domin kafa tata kasa mai cin gashin kanta, abin da ya haifar da fargaba da neman haddasa rarrabuwar kawuna a kasar a lokutan baya. Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyukan kungiyar tare da ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.