Amnesty: Rikicin makiyaya ya halaka mutum fiye da 3,600
December 17, 2018Talla
Rahoton da kungiyar ta fitar a wannan Litinin ya nunar cewa wadannan mutanen sun mutu ne a rikicin da ya auku tun daga shekarar 2016, sai dai ta ce an fi samun asarar rayuka daga rikice rikicen da suka auku a cikin wannan shekarar.
Rahoton ya ci gaba da cewa, rashin daukar mataki na gudanar da sahihin bincike tare da hukunta wadanda aka samu da laifi, na daga cikin dalilan da ke assasa rikici a sassan Najeriya. Masana a nasu bangaren, sun baiyana fargabar barkewar sabon rikici a yayin da ake shirin shiga yanayin rani ganin a wannan lokacin ne makiyaya suke soma yawo da dabbobinsu don samar musu abinci.