Amirka Za ta riɓanya yawan sojojinta a Laberiya | Labarai | DW | 30.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka Za ta riɓanya yawan sojojinta a Laberiya

Amirka ta ce za ta riɓanya addadin sojojinta da ke a Laberiya domin taimaka wa wajen daƙile cutar Ebola da ke yin barazana a yankin yammancin Afirka baki ɗaya.

Tun da farko Amirkan ta aike da sojojinta kusan dubu uku waɗanda za su kula da aikin gina cibiyoyin yaƙi da cutar tare da ba da horo ga sauran jami'an kiwon lafiya da kuma na sa kai

da ya ke yin jawabi a zauren taron Mjalisar Ɗinkin Duniya, ministan harkokin waje na Laberiya ya ce cutar ta Ebola babban bala'i ne. A ƙasar ta Laberiya dai ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane 1830 yayin da a Guinea da Saliyio addadin waɗanda suka cikka da cutar ya kai dubu uku.