Amirka za ta kara sanyawa Iran takunkumi | Labarai | DW | 22.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta kara sanyawa Iran takunkumi

Shugaban Amirka Donald ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta kara kakabawa Iran karin takunkumi biyo bayan harbo jirginta maras matuki da ta yi a 'yan kwanakin da suka gabata.

Shugaban Amirka Donald ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta kara kakabawa Iran karin takunkumi biyo bayan harbo jirginta maras matuki da ta yi a 'yan kwanakin da suka gabata.

Shugaban ya ambata hakan ne dazu gabannin fara tattauna da masu bashi shawara. Ko da dai bai yi karin haske kan irin takunkumin da Amirka din za ta kara kakabawa Iran din ba amma dai ya ce takunkuman suna da yawan gaske. Wannan dai na zuwa ne dadai lokacin da kasashen duniya ke cigaba da kira ga Tehran da Washington kan su yi amfani da hanyoyi na diflomasiyya wajen warware takaddamar da ke akwai tsakaninsu.