Amirka ta yi kashedi ga Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 03.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi kashedi ga Koriya ta Arewa

Kasashen Amirka da Koriya ta Kudu da Japan sun yi wa Koriya ta Arewa kashedi a wannan Laraba a game da yinkurin da take na sake wani gwajin makamin nukliya a nan gaba.

Kasashen Amirka da Koriya ta Kudu da Japan sun yi wa Koriya ta Kudu kashedi a wannan Laraba a game da yinkurin da take na sake wani gwajin makamin nukliya a nan gaba.

Wadannan kasashe sun yi wannan gargadi ne bayan da hukumomin Koriya ta Arewa suka shaida wa wasu jami'an Majalisar Dinkin Duniya aniyarsu ta sake harba makamin mai lizzami mai dauke da taurarin dan Adam tsakanin ranar takwas da ta 25 ga wannan wata na Fabrairu.

Shinzo Abe firaministan kasar Japan ya ce a bayyane take cewa aniyar Koriya ta Arewa ta neman sake harba wani makami mai lizzami ta sabawa kudirin Majalisar Dinkin Duniya kuma wata babbar takula ce dama barazana ga tsaron lafiyar kasashensu, dan haka ya zamo dole ga kasashen duniya da su dauki mataki na tilasta wa koriya ta Arewar yin watsi da shirinta na nukliya

Kasar ta Japan dai ta sha alwashin kakkabo makamin kasar ta Koriya ta Arewa idan har ya kasance barazana ga tsaron lafiyarta