Amirka ta sanya rundunar sojin Iran cikin kungiyar ta′adda | Labarai | DW | 08.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta sanya rundunar sojin Iran cikin kungiyar ta'adda

Shugaba Donald Trump na Amirka, ya sanya rundunar sojin kasar Iran cikin jerin kungiyoyin ta'adda na kasashen waje.

Matakin na Shugaba Trump wani yunkuri ne na kara tsananta wa Iran din, wanda ka iya dagula harkokin diflomasiyyarta a yankin kasashen larabawa.

Wannan ne karo na farko da Amirka ke ayyana gwamnatin wata kasa a matsayin kungiyar ta'adda a duniya.

Tuni kuwa gwamnatin kasar Bahrain, ta yi marhabin da matakin na Amirka.

Matakin ya kuma kakaba takunkumin janye kadarorin da rundunar mayakan juyin juya halin kasar ta Iran ka iya mallaka a wuraren da Amirka ke da iko, da ma katse duk wata hulda da ita.

Sai dai gwamnatin Iran, ta yi barazanar rama wa kura aniyarta.

A shekara ta 1979 ne dai aka kafa rundunar juyin juya halin na Iran, inda take karbar umurni kai tsaye daga jagoran addini na kasar.