Amirka ta lafta wa jami'an Sudan takunkumi | Labarai | DW | 21.03.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta lafta wa jami'an Sudan takunkumi

Amirka ta dauki matakin ladabtar da wasu manyan jami'an 'yan sandan Sudan ta hanyar kakaba musu takunkumin karya tattalin arziki tare da kwace kadarorinsu.

Amirka ta kakaba wa manyan jami'an 'yan sandan kasar ta Sudan sabbin takunkumi na karya tattalin arziki, suna daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifuka da suka keta hakkin bil'adama. Baya ga takunkumin, Washington za ta kwace kadarorinsu da ke Amirka.  

An jima ana zargin rundunar ta musanman mai suna Central Reserve Police (CRP) da aka tanadar don kwantar da tarzoma, da amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zanga da ke adawa da gwamnatin soji. 

Tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a watan Oktobar 2019 aka soma zargin sojojin da yunkurin hana jama'ar kasar 'yancin fadin albarkacin baki. Rayuka da dama sun salwanta a yayin da tattalin arzikin kasar ke barazanar durkushewa a tsawon lokacin da aka kwashe ana fama da tashe-tashen hankula a Sudan.