1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya haramta maziyarta daga Brazil

Abdullahi Tanko Bala
May 25, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya haramta shigar maziyarta daga Brazil yayin da cutar COVID 19 da kuma mace-mace ke karuwa a kasar

https://p.dw.com/p/3ciW4
Brasilien Jair Bolsonaro vor einem Hot Dog Stand
Hoto: Reuters/A. Machado

Fadar gwamnatin Amirka ta sanar da haramtawa matafiya daga Brazil shiga cikin kasarta domin dakile yaduwar annobar corona daga kasar ta kudancin Amirka.

Wannan mataki dai na zama babbar mahangurba ga shugaban Brazil Jair Bolsonaro wanda ke bin sahun shugaba Trump wajen taron gangamin jama'a da rashin martaba tazara a tsakanin juna.

Brazil na da mutane fiye da 347,000 da suka kamu da cutar ta COVID-19 inda a yanzu ta zama kasa ta biyu a duniya bayan Amirka ta cutar ta yi kamari.

Mutane fiye da 22,000 suka rasu a Brazil sakamakon annobar corona a fadin kasar