Amirka ta ce ba za ta bawa Ukraine makamai ba | Labarai | DW | 07.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta ce ba za ta bawa Ukraine makamai ba

Gwamnatin Amirka ta ce ba ta da shirin baiwa Ukraine makamai don tunkarar 'yan aware a fafatawar da ake yi a gabashin kasar ta Ukraine.

Guda daga cikin jami'an gwamnatin Amirkan da ya zabi a saka ya sunansa shi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters hakan, inda ya kara da cewar ko da wasa fadar mulki ta White Housa ba ta yi wannan alkawari ba na bada tallafin na makamai ba.

Kalaman jami'in na Amirka dai na zuwa ne bayan da guda daga cikin ma'aikatan ofishin shugaban Ukraine din ya ke cewar kasarsa da mambobin kungiyar NATO ciki kuwa har da Amirka sun amince da baiwa Ukraine din tallafin makamai da mashawarta ta fuskar soji a taron kungiyar da aka kammala ranar Juma'ar da ta gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal