1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Jim Mattis ya yi murabus

Abdul-raheem Hassan
December 21, 2018

Jim Mattis ya dauki matakin ajiye aiki ne bayan gaza shawo kan Shugaban Donal Trump kan janye dakarun Amirka daga Siriya.

https://p.dw.com/p/3ATFg
James Mattis
Hoto: picture-alliance/AP/C. Kaster

Sakataren harkokin tsaron ya kuma jagoranci zanga-zanga a cikin da wajen Amirka domin nuna adawa da matakin Shugaba Donald Trump na janye sojojin Amirka daga kasashen Siriya da Afganistan ya ajiye aiki. Shugaba Trump ya sanar da janye dakarun Amirka 2,000 a Siriya bayan ikirarin gamawa da mayakan IS tare da ikirarin cewa Amirka ba za ta ci gaba da kasancewa masu gadin kasashen yankin Gabas ta tsakiya ba. Kwararru a fannin tsaro a Amirka sun nuna shakku kan yadda cire sojojin Amirka a Siriya zai shafi martabar Amirka a idanun Kurdawa kawayen Amirka wajen yakar IS a yankin Gaba ta tsakiya.