1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Fatan samun daidaito da Amurka

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
March 15, 2023

Sakataren harkokin wajen Amurka ya bukaci Habasha da ta karfafa zaman lafiya a arewacin kasar da yaki ya daidaita, tare da sanar da shirin bayar da taimako kudin da ya kai dalar Amurkan miliyan 331 ga Habashan.

https://p.dw.com/p/4Ojsj
Habasha | Abiy Ahmed | Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da firaministan Habasha Abiy Ahmed Hoto: Fana Broadcasting Corporate S.C

Wannan dai na zuwa ne, yayin ziyarar da sakataren harkokin kasashen ketare na Amurkan Antony Blinken ya kai, a kasar da ke da nufin sake farfado da alakar da yakin shekaru biyu ya girgiza. Babban jami'in diflomasiyyar Amurkan ya kai ziyara a Habasha da suke dasawa na tsawon lokaci ne a karon farko tun bayan kawo karshen yakin da aka yi a yankin Tigray, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 500 kamar yadda kididdigar Amurkan ta nunar. Hakan dai ya sa Washington ta yanke huldar kasuwanci da kasar da ke zaman ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka.

Karin Bayani: Ministar harkokin wajen Jamus na ziyara a Habasha

Yayin da kasashen Chaina da Rasha ke kara neman tasiri a kasar Habasha da ma nahiyar Afirka, Blinken ya bude ziyarar tasa da bayyana fatan samun kyakkyawar alaka a lokacin da ya ziyarci ma'aikatar harkokin wajen Addis Ababan. Blinken ya ce lokaci ne mai matukar muhimmanci lokaci ne na fata, idan aka yi la'akari da zaman lafiya a arewacin kasar da ke samun ci gaba. Yana mai cewa ya kamata a ci gaba, kuma akwai bukatar karfafa dangantakar da ke tsakanin Amurka da Habasha. Akwai abubuwa da yawa da za a yi amma abu mafi mahimmanci shi ne zaman lafiyar da ke faruwa a arewa.

Habasha | Abiy Ahmed | Anthony Blinken
Ana fatan wannan ganawar, za ta kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashenHoto: Fana Broadcasting Corporate S.C

Sakataren harkokin wajen na Amurka wanda ya yi zargin cewar an aikata laifukan yaki, ya ce manufarsa ita ce karfafa dangantaka da Habashan da ke zaman cibiyar Tarayyar Afirka a daidai lokacin da shugaban Amurka Joe Biden ke kokarin kulla alaka da kasashen nahiyar. Daga bisani Blinken ya gana da Firaminista Abiy Ahmed inda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "Bangarorin biyu sun amince da karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen ta tsawon lokaci tare da kudurin yin hadin gwiwa" a tattaunawar da aka hana manema labarai halarta. Blinken ya kuma bayar da sanarwar sabon taimakon jin kai da ya kai sama da dala miliyan 331 ga Habasha, wacce ita ma ke fama da matsalar fari a yankunanta na kudanci da Kudu maso Gabas.

Karin Bayani:Yara za su shiga halin tasku a kusurwar Afirka

A yayin da ya ke rangadin wata cibiyar ajiyar kayayyakin tallafi ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Addis Ababa, Blinken ya ce wannan tallafin zai taimaka wajen ceto rayukan wadanda tashe-tashen hankula da fari da karancin abinci ya shafa a Habasha. Sabon tallafin wanda ya kawo jimillar taimakon jin kai da Amurka ke yi a Habasha zuwa sama da dala miliyan 780 a cikin kasafin kudinta na 2023, an yi shi ne domin cin gajiyar kowa da kowa a cewar jakadan Amurkan. A Alhamis din wannan makon ne dai Antony Blinken ke isa Jamhuriyar Nijar da ke zama kasa ta biyu, a ziyarar da ya ke yi a wasu kasashen Afirka.