1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwa bayan sulhu a yankin Tigray na Habasha

Ramatu Garba Baba M. Ahiwa
November 29, 2022

Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Habasha da 'yan yankin Tigray, ta soma kawo haske ga rayuwar al'ummar yakunan da yaki na sama da shekara guda ya daidaita.

https://p.dw.com/p/4KEm5
Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Sama da shekara guda aka kwashe ana gwabza fada a tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da 'yan gwagwarmayar neman 'yancin yankin Tigray wadanda ke adawa da manufofin gwamnatin. Duk da cewa an yi nasarar cimma matsaya a yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu, da dama na ganin sai an yi da gaske kafin kasar ta koma daidai a saboda halin rayuwar damuwa da kunci da rikicin ya jefa jama'a a ciki. Bugu da kari, ba a iya mayar da layukan sadarwa da aka  katse a yayin rikicin ba, lamarin da ya bar jama'a cikin halin kunci.

Duk da haka akwai wadanda suka yarda cewa zama lafiya ya fi zama dan sarki, don a karon farko tun bayan barkewar yakin, kwamandan rundunar sojin yankin Tigray Janar Tadesse Werede ya bayyana farin cikinsa kan sasancin da matakin da suke dauka ya samar ta fuskar tabbatar da zaman lafiya.

Äthiopien Tigray-Krieg |  Ayder Krankenhaus in Tigray
Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Kimanin kungiyoyi masu zaman kansu 72 ne suka mara wa yarjejeniyar zaman lafiyan baya, kuma sun kuduri aniyar bayar da taimako ga wadanda suka tafka asara ta dukiya ko rashin dangi ko suka ji rauni a yayin rikicin da kayayyakin agaji da kula da lafiyarsu don rage musu radadi, Daniel Mekonnen daya ne daga cikin jami'an kungiyoyin.

A dai farkon wannan watan na Nuwamba mai karewa aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da bangaren gwamnatin Habashan da na 'yan tawayen TPLF na Tigray a kasar Afirka ta Kudu, kafin daga bisani su amince da mutunta yarjejeniyar a yayin wata ganawa da suka kuma yi a kasar Kenya, kasar da ta shiga tsakani don ganin sun zauna lafiya da juna.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani