1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warware rikicin Habasha da mayakan Tigray

Abdullahi Tanko Bala
January 13, 2023

Jaridun sun yi tsokaci kan ziyarar ministar harkokin wajen Jamus Analena Baeborck da takwararta ta Faransa Catherine Colonna zuwa kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/4M9e5
Äthiopien Annalena Baerbock zu Besuch
Hoto: Fana Broadcasting Corporate S.C.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da Jaridar die Tages Zeitung sun yi tsokaci kan ziyarar ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da takwararta ta Faransa Catherine Colonna zuwa kasar Habasha  domin karfafa dorewar zaman lafiya a tsakanin gwamnatin Habashar dayan awaren.

Kasashen biyu Jamus da Faransa sun gudanar da  shawarwari tare da Firaministan Habasha Abiy Ahmed sannan suka gana da shugaban kungiyar tarayyar Afirk, yin hakan ya kasance babban hobasa na aiwatar da shirin zaman lafiya. A fadan da aka yi a arewacin kasar ta Habasha tun daga watan Nuwambar 2020 Alkaluma sun nuna kusan mutane dubu 500 ne suka rasa rayukansu.

A cikin shekaru biyun gwamnatin Habasha ta toshe yankin na Tigray tare da dakatar da samar da wutar lantarki da sadarwa da kuma zirga-zirgar jiragen sama zuwa yankin.

A yanzu dai sakamakon nasarar yarjejeniyar zaman lafiyar kungiyar TPLF ta amince da kwance damara tare da mika makamanta. Kakakin rundunar sojin Tigray, ya rubuta a shafinsa na twitter a ranar Laraba, cewa suna fata mika makaman zai samar da cigaban da

ake fata na dorewar zaman lafiya.

 

 Senegal na cikin Juyayi shi ne wani sharhi da jaridar  Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi.

Hadarin mozar safa a Senegal
Hadarin mozar safa a SenegalHoto: Cheikh Dieng/AFP

Jaridar tayi tsokaci kan hadarin wasu motocin Bus da suka yi taho mu gama wanda ya jawo hasarar rayukan mutane 39 wasu da dama kuma suka sami raunuka. Hadarin wandaya faru a cikin dare a kan hanyar zuwa Mali ya tada hankali kan yawaitar aukuwar hadura akan hanyoyi wanda aka danganta da gudun wuce sa'a da rashin bin dokokin hanya dawasu direbobin ke yi.

Jaridar ta tunato cewa a shekarar da ta gabata an sami aukuwar haddura 231 da hasarar rayukan mutane kimanin 70.

Jaridar tace  Ayar tambayar ita ce shin ba a baiwa direbobi horo ne? me ya sa ba a karfafa dokokin hanya? me ya sa kuma ba a sa ido akan tsoffin motoci da ake shigo dasu daga waje?

 

Damuwa kan sojojin haya na Rasha a Kwango.

Mayakan tawaye na M23 a Kwango
Mayakan tawaye na M23 a KwangoHoto: GLODY MURHABAZI/AFP via Getty Images

Jaridar Tages Zeitung ta ce samun gawar wani farar fata sanye da kayan soji ya haifar da muhawara a Kwango na kasancewar sojin haya na kamfanin tsarona Wagner na Rasha. Ba ga kasar Ukraine kadai ba dasojin Rasha suke keta haddin bil Adama ba, suna ma aikata hakan a cikin Kongo. Kasashen yamma sun sha baiyana damuwa da ta'asar kungiyar yan tawaye ta M23. Shugaban Kongo Felix Tshisekedi a cikin watan hira ya baiyana cewa basa bukatar sojin haya. 'Yan tawayen M23 dai na zargin cewa Wagner sun shiga kasar ce da sahalewar gwamnatin Kwango.