Trump na shirin dora sabon takunkumi ga Rasha
August 9, 2018Sabon takunkumin za a sanya shi kan Rasha nan gaba a cikin wannan wata, abin da ke zuwa duk da alamun ingantar dangantaka tsakanin Shugaba Donald Trump na Amirka da Vladimir Putin na Rasha da aka fara gani a baya. A cewar ofishin harkokin wajen kasar ta Amirka, mahukuntan na birnin Washington a wannan mako sun amince cewa Rasha ta yi amfani da sinadari me guba a kokarinta na halaka Sergei Skripal da 'yarsa Yulia don haka dole karin takunkumi ya biyo bayan kasar ta Rasha.
Ma'aikatar ta ce an sanar da majalisa a ranar shida ga wannan wata na Agusta don haka takunkumin zai fara aiki a wuraren ranar 22 ga watan nan na Agusta. Takunkumin da zai shafi hana siyar wa Rasha kaya da za su shafi harkokin tsaro kamar yadda wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen na Amirka da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana.