Amirka: Martani kan kutsen magoya bayan Trump | NRS-Import | DW | 07.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Amirka: Martani kan kutsen magoya bayan Trump

Kungiyar Tarayyar Turai da sauran kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani kan kutsen da magoya bayan Shugaba Donald Trump na Amirka suka yi a majalisar dokokin kasar.

USA Das Capitol in Washington während der Großen Depression

Mamayar majalisar dokokin Amirka domin hana amincewa da zaben Joe Biden

Magoya bayan Shugaba Donald Trump dai sun kutsa majalisar dokokin kasar Amirkan da nufin nuna adawarsu wajen tabbatar da nasarar da Joe Biden ya samu a zaben shugaban kasar da ya gabata. Matakin magoya bayan Trump din dai ya janyo daga sassn duniya, inda galibi shugabannin kasashe ke yin tir da shi. A nasa martanin, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce hotunan bidiyo na yadda abin ya faru ya kada jama'a kuma lamarin ya nuna yadda tsarin dimkuradiyya ke cikin garari: "Abubuwan da muka kalla sun nuna mana sakamakon karerayi da raba kawunan al'umma da aka yi da sunan dimukuradiyya. Mun ga kalamai na tunzura jama'a. Wannan wani babban tabo ne ga dimukuradiyya.'' 

Karin Bayani: Shugabanin kasashen duniya na taya Joe Biden murna

Kasar Rasha da ta jima tana samun sabani da Shugaba Trump ta ce wannan ya nuna ke nan daga yanzu bai kamata Amirka ta ci gaba da yi wa wasu fankamar cewa a yi koyi da dimukuradiyyarta ba, kamar yadda shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin kasar ke cewa: "Daga yanzu Amirka ta rasa 'yancin tirsasa wa wata kasa bin tsarin dimukuradiyya, abin kunya ne kwarai.'' 

US-Kapitol | Sturm der Trump-Fans

Magoya bayan Trump sun fasa tagogin majalisar dokokin Amirka domin su kusta ciki

Kawo yanzu dai ana fargabar yamutsin da ya faru ya haddasa mutuwar mutane hudu. Jagoran adawar Burtaniya Keir Starmer ya ce da tun farko Trump ya amince cewa zai mika mulki cikin girma da arziki da ba a kai ga wannan asara ba. A saboda haka ya zama wajibi Trump ya dauki alhakin duk abin da ya faru. To amma yayin da kasashen duniya ke ci gaba da sukar shugaba Trump da magoya bayansa kan lamarin, wasu daga cikin magoya bayan Trump da suka yi kutse a majalisar na cewa hakkinsu suka je nema.

Karin Bayani: Shugaba Trump ka iya lashe zabe

Sai dai duk da irin wannan fassara da magoya bayan Trump ke yi wa kutsen da wasunsu suka yi a majalisar dokokin Amirka, domin hana tabbatar da nasarar zababben shugaban kasar Joe Biden kasashen duniya da dama sun yi takaicin lamarin, inda hatta firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ake ganin suna dasawa sosai da Donald Trump din, a wannan karon ya ce maganar gaskiya an aikata ba daidai ba, yayin da kasar Iran ta ce tana fata Joe Biden zai dauki darasi daga abin da Shugaba Trump ya yi a daidai lokacin da yake gab da sauka mulki.

 

Sauti da bidiyo akan labarin