Amirka da yarjejeniyar nukiliyar Iran | Labarai | DW | 15.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da yarjejeniyar nukiliyar Iran

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce cimma matsaya kan batun nukiliyar Iran ya kawo karshen duk wata dama da Iran din ke da ita wajen mallakar makaman kare dangi.

Obama ya ce da ba su kai ga samun nasarar cimma wannan yarjejeniyar ba, to tabbas zai wahala su dakile yunkurin da Iran din ke yi. Obama ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai gabanin muhawarar da majalisar dokokin Amirkan za ta yi a kan batun wanda ke cike da kalubale. A yayin jawabin nasa dai Obama ya ce yana fatan majalisar za ta gudanar da muhawara bisa nazari da hasashe mai kyau ba bisa siyasa ba. A yanzu dai ana dakon yadda za ta kaya a majalisar dokokin Amirkan da alamu ke nuni da cewa ta yiwu majalisar tai fatali da yarjejeniyar.