Amfanin ziyarar Buhari a Benin | Labarai | DW | 01.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amfanin ziyarar Buhari a Benin

A ci-baba da neman goyyon bayan makwabtansa bisa yaki da Boko Haram, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na ziyarar aiki a Jamhuriyar Benin.

Shugaba Buhari a wannan makwanne ya ziyarci kasar Kamaru cikin matakan da gwamnatinsa ke dauka na hada rundunar sojoji wanda za ta karshen kungiyar Boko Haram. Ko da yake ziyar ta Buhari a Jamhuriyar Benin ta zo dai-dai da bikin cika shekaru 55 da da Benin ta samun 'yanci daga Faransa, amma batun gamayyar sojojin kasashe makobta da za su yaki Boko Haram shi ne gaba a tattaunawar da takwansa na Benin Boni Yayi.