Ambaliyar ruwa ta yi ta′adi a kasar Sudan | Labarai | DW | 03.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a kasar Sudan

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya hallaka tare da raba wasu mutane da dama da muhallansu a Sudan.

Mahukunta a kasar Sudan sun bayar da sanarwar mutuwar mutane 5 inda kuma wasu dubbai suka rasa mahallansu sanadiyar ambaliyar ruwa, inda ambaliyar ta yi awon gaba da gidaje kimanin gidaje sama da 3,500 

Tun a ranar Jumma'ar da ta gabata ce aka tafka ruwan da ya haddasa afkuwar lamarin, a cewar ministan cikin gida na Sudan  Eltrafi Elsdik a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin din nan.