1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan mutanen duniya ya kai bilyan takwas

Uwais Abubakar Idris SB/AH
November 15, 2022

Ana Najeriya na kara rungumar tsarin aure da mace daya lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yawan mutane da suke rayuwa a doron kasa sun kai bilyan takwas.

https://p.dw.com/p/4JYfv
Milyoyin mutane | lokacin zuwa aiki a birnin Lagos na Najeriya
Najeriya ta fi yawan mutane a AfirkaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

A dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa yawan al'ummar da suke a duniya sun kai bilyan 8 a yanzu. A Najeriya ana samun karuwar rungumar tsarin rayuwa na mace daya a tsakanin ‘yan boko da ba sa haihuwa da yawa. Shin me ya sanya karuwar wannan sabon tsari na rayuwa a Najeriyar?

Wannan rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar ya nuna cewa yawan al'ummar da ke rayuwa a doron kasa sun kai bilyan 8 a wannan shekarar, inda aka samu raguwar mutanen da ke mutuwa tare da kari na wadanda ke dadewa a raye. Rahoton ya nuna cewa Najeriya ce kasa ta shida a yawan jama'a a duniya inda take da kashi 2.7 na yawan al'ummar duniya. Hon Nasiru Isa Kwarra shi ne shugaban hukumar kula da yawan jama'a ta Najeriya ya ce yawan jama'a abin alfahari ne ga kasar.

To sai dai ana ganin sauyi na yanayin rayuwa a Najeriyar inda mafi yawa ‘yan boko ke kara rungumar tsari na auren mace guda tare da raguwar yawan yaran da suke haihuwa musamman wadanda ke zaune a alkarya. Shin me key a sanya samun karuwar wannan nau'I na rayuwa a tsakanin ‘yan boko ba tare da la'akari na al'ada ko addini ba a Najeriyar? Dr Hussaini Tukur masanin a fanin ci gaban alumma da tsare-tsare a jami'ar jihar Nasarawa, wanda yake cewa duk da yake rahoton ya nuna raguwar mutuwar jama'a amma a Najeriya ana samun karuwar kashe-kashen jama'a saboda rigingimu na ‘yan bindigar daji da ta'adanci da aka kwashe fiye da shekaru 10 ana fafatawa.

Duk da karuwar yawan a'lumma a Najeriya a yanzu, hukumar kula da hayaiyafar jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta ja hankali a kan batun haihuwar da ba a shirya bag a mata. A yanzu dai yawan jama'ar duniya da ya kai bilyan takwas ya nuna cewa fiye da yawan wannan adadi suna zaune ne a kasashe takwas na duniya da suka hada da Inidiya, Pakistan Najeriya da sauransu. An yi hasashen kasar Indiya za ta zarta China a yawan jama'a a shekara ta 2023.